Shin Masu Safarar Mutane Sun Fi Karfin Gwamnatin Najeriya Ne?

Yara kanana irin wadanda ake safararsu zuwa kasashen waje irinsu Saudiya

Har yanzu ana safarar yara mata kanana zuwa Saudiyya da sunan samar masu aiki amma a zahiri ana saka su aikin bauta lamarin ya ci gaba duk da cewa an sanar da mahukuntan Najeriya

Safarar mutane, musamman yara kanana daga Najeriya zuwa kasashen waje irin su Saudiyya ta zama ruwan dare gama gari.

Muryar Amurka ta yi kichibis da wani Idris Salman Muhammad a kasar Saudiya, wanda ya taba yana cikin masu safarar mutane kamin dga bisani yayi nadama, ya ce ya yi kimanin shekaru 15 yana aikin. Yakan kawo mutane da sunan samar masu aiki amma a gaskiya bautar dasu a keyi.

Irin ukubar da mutane ke sha ana bayyana su ta kafofin yada labarai da yanar gizo domin mutane su gani.

Wani ma da ya yi fiye da shekaru 40 a kasar Saudiyya, Muhammad Tari, y ace abubuwan da ake yi ba daidai ba ne. Ana kawo yara maza da mata da sunan basu aiki a biya su kudin kasar dubu biyu ko uku, amma a zahiri bauta su keyi irin na bayin da.

An dade ana safarar ‘yan Najeriya zuwa wasu kasashe ba tare da mahukumtan kasar sun dauki kwararan matakai ba.

Muryar Amurka ta tattauna da karamin jakadan Najeriya Ambassador Muhammad Sani Inusa dake Birnin Jeddah, domin sanin ko hukumomin kasar na sane da abun dake faruwa.

A cewar Ambassador Inusa, wadanda suka shiga kasar da sunan yin aiki halin da suka samu kansu ciki bashi da dadi. Rahotannin da suke samu baa bun nanatawa bane. Yace ta dalilin haka ne ya tura wasu jami’ansa biyu zuwa wani wurin da aka kawo wasu yara mata kanana ana wulakantar dasu. Jami’an sun samu kamfanin da ya kawosu kuma sun aika da rahotanni akan halin da ‘yan Najeriya ke ciki a Saudiyya, amma har yanzu ba’a dauki wani mataki ba.

Ambassador Inusa y ace suna bukatar a dakile lamarin tun daga Najeriya, kada ‘yan matan su bar kasar.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da cikakken bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Masu Safarar Mutane Sun Fi Karfin Gwamnatin Najeriya Ne? - 7' 10"