Shugabannin bangaren ‘yan adawa na jam’iyyar Democrat masu rinjaye a majalisar wakilan Amurka, sun gargadi Fadar gwamnatin ta White House, da su kwan da shirin cewa za a aiko masu da takardun neman su gabatar da takardun da suka shafi huldar Shugaba Trump da kasar Ukraine.
A lokacin da wani dan jarida ya tambayi Shugaba Trump a wani taron manema labarai, shin ko zai mika wuya ga wannan bukata ta majalisar wakilai wadda ta kaddamar da bincike da mai yiwuwa ya kai ga tsige shi, sai Trump ya ce, “shi ai ya saba ba da hadin kai.”
A jiya Laraba, shugaban kwamitin kula da harkokin tattara bayanan sirri a majalisar wakilan, Adam Schiff, ya ce duk wani yunkuri da gwamnatin Trump ta yi na kawo cikas a wannan bincike, za su kalle shi a matsayin shaidar hana doka ta yi aikinta
A daya bangaren kuma, a yau Alhamis ake sa ran tsohon jakadan Amurka na musamman kan Ukraine, Kurt Volker, da ya ajiye aikinsa a makon da ya shude, zai bayyana a gaban kwamitocin majalisar domin yin bayani kan irin rawar da ya taka a huldar Shugaba Trump da Ukraine.
Ana dai zargin Trump da laifin neman taimakon shugaban Ukraine Zelenskiy, wajen bankado wata badakala da ake zargin dan tsohon mataimakin Shugaba Amurka, Joe Biden – wato Hunter Biden da aikatawa, da nufin samun makamin da zai bata sunan Biden da ake hasashen da shi zai kara a zaben 2020.