Shin Da Gaske Tinubu Ya Ce Gwamnan CBN Cardoso Ya Yi Murabus?

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso

A 'yan kwanakin nan, rahotanni na cewa Cardoso na fuskantar suka saboda rashin iya shawo kan kalubalen tattalin arziki da kuma daidaita darajar Naira.

Fadar Gwamnatin tarayya ta musanta rahotanni da ke cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Gwamnan Babban Bankin kasar na CBN Yemi Cardoso ya yi murabus daga mukaminsa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta kafar X, mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya musanta rahotannin da ke cewa Tinubu ya umarci Cardoso da ya yi murabus.

A 'yan kwanakin nan rahotanni na cewa Cardoso na fuskantar suka saboda rashin iya shawo kan kalubalen tattalin arziki da kuma daidaita darajar Naira.

‘Yan Najeriya na fama da hauhawar farashin kayayyaki a watannin nan, ko da yake, hukumar gididdiga ta NBS ta ce farashin kayayyaki na sauka a hankali.

A takaitacciyar sanarwar tasa a shafin X a ranar Talata, Onanuga ya bayyana rahoton a matsayin “mara tushe.”

“Duk karya ne. Shugaba Tinubu bai bukaci Yemi Cardoso ya yi murabus ba,” in ji Onanuga yayin da yake kore rahoton.

A watan Satumbar 2023, Shugaba Tinubu ya nada Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin kasa, inda ya maye gurbin Godwin Emefiele da ke fuskantar tuhume-tuhumen wurare kudaden kasa da daukar nauyin ayyukan ta’addanci – tuhume-tuhumen da ya musanta.