Shin Gaskiya ne Miliyan 150 Yayi Batar Dabo a Jihar Neja

Jam’iyyar APC da Gwamnatin Jihar Neja Sun Shiga Rudani a sakamakon Wani labarin da aka baza dake Nuna cewa Naira Milyan 150 tayi batan dabo a gidan Gwamanatin jihar.

Wasu kafafen yada labarum Najeriya, ne dai suka ce sun jiwo kakakin APC, a jihar Neja, Mr. Jonathan Vatsa, yana kira ga Gwamna Abubakar Sani Bello, da ya hanzarta lalubo wasu kudade har Naira Miliyan 150, da aka ce sun bata a gidan Gwamnatin jihar Neja.

Duk da yake dai jam’iyyar ta APC dama Gwamnatin jihar Nejan sun karyata wannan labara tuni ‘yan siyasa masamman na bagaren adawa suka fara maida martini.

Da farko dai kakakin APC, a jihar Neja, Mr. Jonathan Vatsa ne ya fara musanta labarin, sakataren yada labarai na Gwamna jihar Neja, Dr. Ibrahim Doba, yace bai san inda wannan labara ya fito ba.

Ko a watan Yuni da ya gabata ma’aikatan Gwamnatin jihar Nejan sun samu kansu cikin wani yanayi na rudani a sakamakon yanda aka zaftare masu kudaden albashinsu na wannan wata, amma Dr. Ibrahim Doba, yace an dauki mataki na maida kudaden kuma an daina.

Tuni ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, suka fara maida martini akan wannan batu Yahaya Ability, tsohon mataimaki na masamman ga tsoho Gwamna Mua’zu Babangida Aliyu, yace da kansu suke tuntube da juna wasu daga cikinsu kuma suna fitowa suna karyatawa, amma shawara itace menene za’a yi da ya dara na Gwamnatin da ta gabata.