Shiga Yanar Gizo Batare da Biyan Ko Kwabo ba

Sama da mutane miliyan 100 a Najeriya basu da hanyar shiga yanar gizo, a dalilin rashin wadatattun kayayyaki da na’urorin baza ta, wadanda kamfanonin waya ke samarwa kuma, suna da tsada da rashin tabbas.

Domin taimakawa mutane WiderNet, kungiya mai zaman kanta a Amurka ta kawo fasahar gina dakin karatun da za' a iya shiga da na’ura batare da anyi amfani da shiga yanar gizo ba, kuma batare da biyan ko sisin kwabo ba.

Jami’ar Ahmadu Bello na ‘daya daga cikin makarantun da ‘dalibai basa samun wadatar yanar gizo, hakan ne yasa WiderNet ta kafa wannan fasahar a makarantar.

Ana amfani da wannan fasaha wajen tura miliyoyin kayan karatu ko bincike daga nesa zuwa cikin dakin karatu na jami’ar, daga nan kuma dalibi na iya zuwa ya karanta ko yayi kofensu cikin na’urarsa, ba tare da ya biya kudi ba.

Daliban jami’ar dai sun nuna jin dadin su ga wannan fasaha musammam ma yadda ya zamanto hanya mafi sauki garesu wajen samun kayayyakin karatu, matsalar wutar lantarki da ake fuskanta itace kawai zata hana ‘dalibai cin moriyar wannan fasaha.