Shettima Ya Tafi Taron Majalisar Dinkin Duniya A Amurka

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima (Hoto: Facebook/Kashim Shettima)

Taron na bana za a gudanar da shi ne daga ranar 24 zuwa 28 ga Satumba, 2024 a birnin New York.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 79.

Shugaba Bola Tinubu ne ya umurci Mataimakin Shugaban Kasa da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa wannan babban taro na kasa da kasa, yayin da shi kuma zai mayar da hankali kan magance matsalolin cikin gida masu muhimmanci, ciki har da bala’in ambaliyar ruwa da ta faru kwanan nan.

“A yayin zaman taron, Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya, ya kuma halarci muhimman taruka a gefen taron, tare da gudanar da tattaunawa da wasu kasashen duniya.” Wata sanarwar dauke da sa hannun kakakin Tinubu na musamman kan sha’anin yada labarai Stanley Nkwocha ta ce.

Taron na bana za a gudanar da shi ne daga ranar 24 zuwa 28 ga Satumba, 2024 a birnin New York.