A baya Jihar Filato ta yi fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini amma an zo an samu saukin lamarin na wani lokaci. Babban darektan hukumar Joseph Lengman ya ce karin fahimtar kan abubuwan da ke haddasa rikici a jihar ya taimaka wajen samar da zaman lafiya na kusan shekaru biyu da rabi kafin abubuwa suka sake tabarbarewa.
Lengman ya ce wannan rikicin da ya auku wani tuni ne domin muddin ba magance abubuwan da ke jawo tashin hankali a jihar ba to sai abin da hali yayi.
Ya kuma ja hankalin hankalin jama'a kan gujewa zubda jini,
"Gaskiya ya kamata mutane su yi tunani a ga yadda za a zauna, a duba, a yafewa juna, mu kuma gyara domin mu yi zaman tare, mu kuma samu zaman lafiya na kwarai a wannan jihar." inji shi
Sannan ya shawarci duba tsarin wanzar zaman lafiya wato 'Plateau Roadmap to Peace' da Shugaba Buhari ya kaddamar a yayin ziyararsa jihar a watan Maris ya zama turbar samar da zaman lafiya a jihar.
Sakataren watsa labarai da hulda da jama'a na Jama'atu Nasril Islam, Umar Faruk Musa, ya ce an dauki matakai da dama don ganin an samu zaman lafiya amma sai wannan lamari ya zo ba ta lissafi.Ya ce akwai tsare-tsaren da gwamnati ta tanadar idan aka tabaka ko aka bata maka, akwai hanyoyin da zaka bi wajen isar da korafinka don a bi ma hakkinka. Amma sai ga jama'a sun koma daukar matakan hukunci da hannunsu wanda ba daidai ba ne ba.
"Babu wani addinin da zai ce maka an baka dama a matsayinka na dan adam wai dauki mataki da hannunka."
Wani masanin tsaro, Toyin Adesina ya ce lokaci ya wuce da za a sakarwa hukumomin tsaro komai su kadai na batun tsaro.
"Duk inda kaga wani abu da bai dace ba na faruwa to a yi maza akai rohoto." inji shi
Saurari rohoton Zainab Babaji
Your browser doesn’t support HTML5