Shawarar Hukumar Lafiya Ta Duniya Game Da Cutar ZIKA

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce ta canza shawarar da ta kan bayar game da kwayar cutar Zika, ta na mai shawartar matafiya cewa duk wanda ya je wurin da ake fama da cutar, to ya yi kaffa-kaffa game da jima'i, ko kuma idan ya baro wurin ya kaurace ma jima'i na tsawon watanni 6.

Hukumar Lafiyar Ta MDD, ta fito da sabon bayanin ne jiya Talata, bayan da ta kwaskware bayanin da ta fito da shi a watan Yuni, wanda ke shawartar maza da su yi kaffa-kaffa da jima'i din, amma su kaurace ma jima'a na tsawon makonni 8 kawai, bayan dawowa daga wurin da ake fama da cutar ta Zika.

Wannan sauyin na zuwa ne yayin da bayanai ke ta nuna yadda cutar Zika, wadda sauro ne ke yada ta, na iya yaduwa daga mutum zuwa mutum.

A Latin Amurka an ga alaka tsakanin wani nau'i na Zika da rashin dacen haihuwa, a jariran da mata masu dauke da cutar ta Zika su ka haifa.