Yace babban manufar su ita ce samar da wata manufa ta kasa da kasa wanda zai ciyar da dankon zumuntar dake tsakanin su a matsayin kasashe ,musamman da kasa kamar Amurka wadda ta dade suna hulda a tsakanin su.
Kafin dai ya wuce wurin taron a ranar Littini, Durtete ya gargadi shugaba Obama cewa kar yace zaiyi masa wani jawabi akan yadda zai yaki masu safarar miyagun kwayoyi wanda yayi dalilin mutuwar mutane dubu 2 masu wannan mummunar sana'ar tun daga lokacin da ya kama ragamar mulki.
Durterte yace wajibi ne ka zama mai ladabi, kar kayi mani kowace irin tambaya, Sai dai yayi anfani da kalamai mara sa dadi da harshen su ga shugaba Obama.
Da farko dai Shugaba Obama bai dauki kalaman na Durterte da muhimmamci ba sa'ilin da yake wa manema labarai jawabi ya bayyana Duterte a matsayin mutun mai son ba’a amma kuma daf ga bisani sai fadar White House tace shugaba Obama ya soke shirin ganawa da Duterte din, maimakon hak zai tattauna ne da shugaban Koriya ta Kudu.
Sai dai kuma sanarwar da ta fito daga Duterte ta bayyana nadamar sa bisa kalaman da yayi na batanci game da shugaba Obama wanda ya haifar da cece kuce, yace yana fatan samun wani lokaci na musammam da zai tattauna da shugaba Obama domin kawo karshen wannan batu.