Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Shiga Sahun Kasashen da Suka Damu da Tashin Hankalin da Ya Biyo Zaben Gabon


Shugaban Faransa Farncois Hollande da Shugaban Gabon wanda aka ce shi ya sake lashe zaben kasar
Shugaban Faransa Farncois Hollande da Shugaban Gabon wanda aka ce shi ya sake lashe zaben kasar

Prime Ministan kasar Faransa Manuel Vall yabi sahun sauran shugabannin duniya wajen bayyana damuwar sa game da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kasar Gabon.

Prime Ministan yana Magana ne sailin da yake tattaunawa da manema labarai.

Vall yace me zai hana a sake kidaya kuriun tunda shugaban ‘yan adawa yayi zargin cewa anyi magudi wajen kidayan su.

An samu gardama da shakku cikin kamar yadda masu sa ido daga kasashen Turai da suka ga yadda zaben a cikin kasar ya kasance musammam akan sahihancin sa, Vall yace don haka yana da kyau a sake kidaya wa.

A cikin satin data gabata ne Hukumar zaben kasarGabon din ta bayyana shugaba Ali Bango a matsayin wanda ya lashe zaben akan abokin karawarsa Jean Ping da kuriu dubu biyar, wannan dai ya haifar zanga-zanga wanda hakan kuma yayi dalilin mutuwar mutane 6.

Yanzu haka Ministan Sharaa na kasar Seraphin Moudounga ya ajiye aikin sa sakamakon zaben na shugaba Ali Bango.

Ministan dai shiune babban jamii na farko a cikin Gwamnatin kasar da ya ajiye aiki sakamakon wannan zaben.

Moundounga ya fada wa gidan Radio Faransa cewa gwamnati tayibiris da bukatun yadda za a samar da zaman lafiya, yace wannan yasa ya ajiye aiki.

Haka kuma shugaban ‘yan Adawa, Ping ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Gabon din kuma yayi kira da a gudanar da yajin aiki, yace muddin harkokin tattalin arzikin kasa ya durkushe hakan zai tilasta gwamnati yin abinda ya dace.

Sai dai rahotanni su bayyana cewa mutane kalilan ne suka yi zaman su gida, domin ko Bankuna da Shaguna a babban birnin kasar Librevile sun bude kuma sun gudanar da harkokin su, wasu ma cewa suka yi basu ji wannan sanarwan ba.

XS
SM
MD
LG