SHARHIN AMURKA: NATO Mai Cike Da Karsashi, Bayan Shekaru 4

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blkinken

A jawabinsa yayin taron ministocin wajen kasashen kawancen tsaro na NATO a birnin Brussels, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce a cikin shekaru 4 da suka gabata, “kawancen ya gudanar da sauye-sauye da karfafawa mafi muhimmancin da aka shafe tsawon shekaru ba a ga irinsu ba”

“Yanzu NATO ta kara girma, ta kuma kara karfi, tana da karfin tattalin arzikin tunkarar duk wani kalubalen dake gabanta. Yanzu NATO nada sabon salon gudanar da tsare-tsarenta.

Ta ayyana kasar Rasha a matsayin babbar barazanarta ta kai tsaye, sannan ta sake haskaka bigiren tsaron da take gudanar da harkokinta a ciki da barazanar da take fuskanta daga kasar China, da kalubale tsakanin kasashe-daga sabbin fasahohin zamani da sauyin yanayi da kuma ta’addanci.”

Sakatare Blinken ya kara da cewar a shekarar 2020 kasashen nato 9 sun cika alkawuran da suka dauka na kashe kaso 2 cikin 100 na arzikinsu akan tsaro, a yau kasashen sun zama 23. Har ila yau, Blinken ya kara da cewa, da shigowar kasashen Finlanda da Sweden, kawancen ya kara samun karfin tunkurar rayuwa anan gaba.”

“Haka kuma kawancen ya kara karfafa tsaro da kariyarmu daga hare-hare. Mun ninka yawan da muke dashi a tungarmu ta gabas. Mun sabunta tsarin gudanar da rundunoninmu…..mun jaddada karfinmu a dukkanin fannoni, ciki harda fagen amfani da fasahar sadarwar intanet data sararin samaniya.

Wadannan jajirtattun kudurori da jari da muka zuba zasu samarwa al’ummominmu tsaro nan da shekaru da dama masu zuwa.”

Alama mafi girma ta hadin kai da jajircewar kawancen NATO shine irin tallafi babu gajiyawa da kasashen dake cikin kawancen suke baiwa Ukraine tun bayan mamayar da Rasha ta yi mata, a cewar Sakatare Blinken; haka kuma ita ce alama mafi girma ta daukar dawainiyar juna. inda Amurka ke samarda gudunmowar dala bilyan 102 ga Ukraine, su kuma sauran kasashen dake cikin kawancen da hukumomin bada agaji su samar da dala bilyan 158.

“Zamu ci gaba da taimakawa wajen tabbatar da cewar Ukraine nada wadatattun kudade da harsashai da dakarun da take bukata domin cigaba da fafatawa zuwa badi-ko kuma ta iya shga tattaunawar sulhu, amma daga matsayi mai karfi.”

“Muna cikin wani lokaci mai matukar mahimmanci ga kasar ukraine da kuma muradan da aka gina wannan kawance na kasashen arewacin tekun atlantic,” a cewar Sakatare Blinken.

“An kafa kawancen nato ne bayan yake-yaken duniya guda 2 a matsayin wani bangare na jerin hukumomin da aka kirkira domin ganin mun kaucewa sake tsunduma cikin wani yakin duniyar.”

“Karfafar NATO,” a cewar Sakatare Blinken, na nufin samun karin karfin dakile hare-hare, da kawancen da zai haifar da sakamakon tunkarar kalubalen dake gaba da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankalin da za su baiwa al’ummarmu damar yin rayuwa yadda ya dace.”

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.