“A yankin Darfur, a baya-bayan nan ma a jihar Al-Gezira, rahotanni na nuni da mummunar karuwar da bazuwar kashe-kashe masu alaka da kabilanci da munanan laifuffukan da (‘yan tawayen RSF) ke aikatawa. haka kuma a yankin Khartoum, hare-haren bama-bamai ta sama da (rundunar sojin Sudan) ke kaddamarwa a kan kasuwannin da wuraren taruwar jama’a ba tare da wata manufa ta soji ba, sun hallaka dimbin farar hula.”
Sakamakon kazantar halin da ake ciki a Sudan, Amurka na da manyan bukatu guda 4.
“Na farko, hakki ne da ya rataya a wuyan dukkanin bangarorin dake cikin rikicin su kyale kayan agaji su ratsa ta kan iyakokin da suka hada Sudan da sauran kasashe da kuma ta hanyoyin da suka hade yankunan kasar,” kamar yadda jakada Thomas Greenfield ta jaddada.
“Muna yabawa hukumomin Sudan akan sake bude mashigar kan iyakar Adre a tsakiyar watan Agustan daya gabata.
Wannan hanya daya tilo ta baiwa kungiyoyin bada agaji damar shigar da wadataccen kayan abinci dana kiwon lafiya da kayayyakin cimakar da zasu wadaci fiye da mutane milyan 1.9.
Yanzu, ya zama wajibi hukumomin sudan su bar mashigar kan iyakar Adre a bude har illa masha-allahu. Milyoyin rayuka ne suka dogara akanta.”
Matak na 2 shine kawo karshen tashe-tashen hankula, a cewar jakada Thomas-Greenfield:
“Kamata yayi dukkanin kasashe su dakatar da bada tallafin soja ga bangarorin dake rikici da juna. Kuma wajibi ne kowannenmu yayi matsin lamba ga bangarorin su koma kan teburin tattaunawa da nufin kawo karshen rikicin.”
“Haka kuma Amurka “na goyon bayan kafa tsarin tabbatar da kiyayewa da sanya idanu da tantancewa biyo bayan samun yarjejeniyar dakatar da rikicin,” a cewar jakada Thomas-Greenfield:
“Irin wannan tsari na iya tabbatar da cewa ana mutuntawa tare da aiwatar dokokin bada agaji na kasa da kasa da yarjejeniyar da aka cimma a jeddah, don haka kamata yayi wannan kwamiti dama al’umma duniya baki daya, su tallafawa kawayenmu na Afrika akan kafa irin wannan tsari, ciki harda tallafi akan tsare-tsaren taswirar yadda za’a aiwatar da yarjejeniyar da yadda za’a tura jami’ai.”
A karshe, ya zama wajibi a kan al’ummar duniya ta bada tallafi wajen komawa kan tafarkin dimokradiyar da farar hula zasu jagoranta wacce za ta kunshi kowa. Hakan kuma zai kunshi neman hakkin laifuffuka da cin zarafin da aka aikata a shekara daya da rabin da ta gabata.
“Akwai bukatar mu a matsayinmu na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya mu ci gaba da yiwa bangarorin dake rikici da juna matsin lamba a kan su dakatar da fada yanzu,” kamar yadda jakada Thomas Greenfield ta ayyana, sannan “su tabbatar da cewa kayayyakin agaji sun kai ga mutanen dake cikin tsananin bukata
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayin Gwamnatin Amurka.