Blinken ya ce karshen annobar “wani lokaci ne dake bukatar yin gagarumin garanbawul akan yadda muke tunkarar taimakekeniya akan mas’alolin da suka shafi tattalin arziki da fasaha.”
“A Amurka, mun fara da zuba gagarumin jari a kan bukatarmu ta kere sa’a.”
“Anan yankin kasashen Asiya da Pacific, mun karfafa alaka mai kusurwa 3 da kasashen Japan da Korea. Mun yaukaka dangantaka mai turaku 4 tsakaninmu da- Indiya da Japan da Austreliya da kuma kawancen bunkasa arzikin kasashen yankin Asiya (ASEAN). Mun kuma kyautata alakarmu da kasashen Vietnam da Indonesia.
“Mun kaddamar da tsarin bunkasar tattalin arzikin Indo-Pacific, inda muka hado kan kasashen 14 - kusan kaso 40 cikin 100 na tattaln arzikin duniya - domin bada kariya ga tsarin kasuwancinmu da yaki da rashawa da kuma komawa amfani da makamashi mai tsafta.”
A lokaci guda kuma, “mun zurfafa tattaunawar da kawancen kasashen APEC, ciki har da marabtar da dama daga cikinku a birnin San Francisco a bara, inda muka samu sabbin yarjeniyoyi masu mahimmanci domin samar da rayuwa mai cike da karsashi da dorewar al’amura ga dukkanimu a nan gaba.”
“Zuwa shekarar 2021, harkokin kasuwancin Amurka sun zuba jarin fiye da dala tiriliyan 1.4 a tattalin arzikin kasashen APEC, abin da ya mayar da Amurka ta zamo hanyar zuba jari kai tsaye a kawancen na APEC”
“Har ila yau kuma, kawancen kasashen APEC ya zuba jarin dala tiriliyan 1.7 a Amurka-daga bangaren makamashi mai tsafta zuwa sinadaran harhada na’urori-inda suka tallafawa guraben ayyukan yin Amurkawa milyan 2.3,” a cewar sakatare Blinken.
“Wannan adadi yana kara bunkasa har kullum. Tun tuni suke kara habbaka a duk shekara, har kullum girma suke yi, ina ganin suna bada wani muhimmin labari ne.”
“Mai yiyuwa zuba jarin ketare kai tsaye zai zamo mafi cancantar ma’aunin gane amana da jajircewa a nan gaba. Bangaren ‘yan kasuwa ba zai zuba kudadensa ba tare da samun amana da jajircewa ba. Ina mai matukar alfaharin cewar mun mayar da Amurka wacce ta fi zubawa da kuma karbar-jarin ketare na kai tsaye a fadin duniya.”[end act]
A karshe, “mun yi kokari wajen shigo da al’ummomin da aka mayar saniyar ware-irinsu mata da ‘yan mata, da al’ummomin yankuna na asali, irinsu ma’aikatan bangarorin da babu ruwansu da gwamnati,” a cewar sakatare Blinken.
“Muna godiya ga kungiyoyi irin kwamitin bada shawarwarin kasuwanci na APEC saboda fifikon daya baiwa wannan aiki tare da kalubalantar gwamnatotci da kamfanoni masu zaman kansu su kara zage damtse wajen fadada ddamar. Ba wai kawai saboda shine abin da ya dace a yi ba, a’a sai dai saboda yankunanmu da kasashenmu za su fi karfi da samun daidaito idan muka baiwa dukkanin al’ummomin dama,” a cewarsa.
“Kuma a karshe, dukkanin lamuran na komawa ne zuwa ga, al’ummominmu. Bukatunsu, da burakansu.”
Wannan sharhi ne da ke nuna ra’ayoyin Gwamnatin Amurka