SHARHIN AMURKA: Kokarin Blinken Na Farfado Da Diflomasiyar Amurka

Antony Blinken yana aiki a cikin jirgin sama daga Doha zuwa London, Oktoba 24, 2024

Gasar kasa da kasa na nan tafe domin bude sabon shafi a al’amuran duniya, a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, a jawabin daya gabatar ga cibiyar harkokin ketare ta kasar

A lokaci guda kuma “har yanzu akwai ragowar dadaddun kalubale da suka hada da-rikice-rikice da ta’addanci da rikita-rikitar siyasa. muna ganin hakan a fadin duniya, daga gabas ta tsakiya zuwa sudan da Venezuela.”

“A halin yanzu, a kokarin shawo kan wadannan matsaloli ta matsaya mai karfi, mun zuba gagrumin jari a nan cikin gida domin cimma manufofinmu kuma muna kokarin sake tattaunawa da farfadowa tare da sabunta kawance da hadin gwiwar da muke dasu a fadin duniya.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kafa hukumar tsaron intanet da manofofi akan fasahar zamani da ofishin jakadan musamman akan muhimmai kuma sabbin fasahohi. “Mun tattaro fasihan mutane a wadannan fannoni domin tabbatar da cewa Amurka da kawayenta sun ci gaba da yin fintinkau a harkar fasahohin dake fasalta rayuwarmu ta nan gaba,” a cewar sakatare blinken.

“A dukkanin inda muke da alakar diflomasiya a fadin duniya, muna bada fifiko ga jagoranci a kan al’adu da kyautata tsari, tare da dabbaka ‘yancin fasahar sadarwar zamani, da bada kariya ga fasahohinmu masu matukar mahimmanci, da kuma mayar da harkokin sarrafa al’amura su zama masu kwari da juriya.”

A lokacin annobar korona, ma’aikatar harkokin wajen ta kirkiri ma’aikatar tabbatar da tsaro a harkar kiwon lafiyar duniya da nufin karfafa tsarin kiwon lafiya, domin yakar miyagun cututtuka, tare da kare afkuwar nau’ukan annoba a nan gaba.

Ma’aikatar wajen ta maida hankali wajen bunkasa ci gaban al’umma da karfafa tsarin sarrafa al’amura da daukaka matsayin ofishin kula da takunkumai, tare da samar da jami’in kula da yaki da cin hanci da rashawa na duk duniya, na cikin jeren abubuwan da aka kirkiro.

Ajandar ma’aikatar wajen ta tafiya da zamani ne ya sanya al’amuranta ke tafiya yadda ya dace, a cewar Sakatare Blinken.” Muna matukar kokarin karfafa dangantakarmu da yin gogayya da manyan abokan hamayyarmu (tare da) cikawa al’umarmu alkawura a lokutan manyan kalubale.”

Hakan ta baiwa Amurka da kwayenta, dangane da China, damar samun muhimmin kawancen da ba’a taba tsammani ba cikin ‘yan shekarun da suka gabata, a cewar Sakatare Blinken.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta kuma fadada damammaki ga kasashe domin samun kudaden raya kasa ta hanyar yin garanbawul ga tsarin bankunan duniya tare da samar da sabbin manufofin bada lamuni.

Jami’an diflomasiyar Amurka na tsara dokoki da ka’idoji ga sabbin fasahohi irinsu kirkirarriyar basira, a daidai lokacin da suke fadada damar cin gajiyar fasahar ga kasashen Tsibiran Pacific dana nahiyoyin afrika da kudanci amurka dama sauran sassan duniya.

Amurka na sake farfado da matsayin jagorancinta a Majalisar Dinkin Duniya, tare da sake komawa cikin kungiyoyi irinsu majalisar kare hakkin dan adam da hukumar kare tarihi da al’adu ta MDD (UNESCO).

“Wadannan cigaba, dama wasu da dama,” a cewar Sakatare Blinken, “na nuni da iko da manufar sake farfado da diflomasiyar Amurka.”

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.