Shaidu Sun Musanta Bayanin Jami'an Tsaro A Abuja

Wasu daga cikkin wadanda ke zaune a gidan da aka kai ma farmakin sun ce da tsakar dare jami'an tsaro suka far ma gidan da harbe-harbe
Mazauna wani makeken gidan da jami'an tsaro suka kai farmaki har suka kashe mutane fiye da goma ciki, sun musanta bayanin da hukumomi suka bayar na yadda aka yi harbe-harbe tare da kisa, su na masu fadin cewa haka siddan da tsakar dare dakaru suka far ma gidan da harbe-harbe.

Wani mazaunin gidan, wanda bai yarda a fadi sunansa ba a saboda fargabar abinda ka iya faruwa gare shi, yace akwai mutane masu yawan gaske cikin wannan gidan, dukkansu talakawa masu aikin sayar da ruwa, ko masu tallar kaya cikin keken kura (Wheel-barrow) da kuma masu tuka keken NAPEP.

Shaidan yace tun da ya ke wannan gidan, bai taba ganin an yi wani taro cikinsa ba, haka kuma bai taba ganin wani abu da zai nuna cewa akwai 'yan Boko Haram ko wasu masu aikata laifi cikin wannan gidan ba.

Yace karar harbe-harben da suka ji ta sa suka fara fita da gudu ta ko ina daga gidan, kuma duk wanda dakarun suka yi ido hudu da shi sai su bude masa wuta. Yace sun fito su biyu da gudu, sai aka harbe wanda yake gaba da shi ya fadi ya mutu a wurin, shi kuma sai ya kwanta a kasa da aka bude masa wuta.

Yace jami'an tsaron da suka biyo ta wurin sun harbe shi a kafa, suka wuce suka bi sawun wadanda ke bayansa.

Ita dai hukumar tsaron cikin gida ta Najeriya ta SSS, ta ce jami'anta sun je wurin ne su na binciken makamai da suka ji labarin an boye a wani wuri kusa da nan.

Wata sanarwar da ta bayar, ta ce, "'Yan Boko Haram sun bude wuta a kan jami'anta a lokacin da suka fara tono wadannan makamai da aka ce an boye. Wasu mutane sun ji rauni, an kuma kama wasu 12 dangane da wannan lamarin."

Amma wannan shaida, da kuma wasu mutane biyar mazauna gidan da suka yi magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, duk sun ce ba haka abin ya faru ba.

Ga bayanin da wannan shaida ya ba wakilin VOA Hausa, Nasiru Adamu el-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Shaidu A Abuja Sun Musanta Bayanin Da Jami'an Tsaro Suka Bayar - 2:00