Dukkanin kasashen 2 na ikirarin cewar yankin Abyei, mai arzikin man fetur, nasu ne.
An kuma samu yaduwar makamai sanadiyar rikicin, inda kungiyar ‘yan tawayen RSF ta shiga yankin na Abyei. Har ila yau, kwararar ‘yan gudun hijira ya sake tagayyara tattalin arzikin Sudan ta Kudu dake cikin mawuyacin hali.
Rundunar jami’an tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta wucin gadi dake Abyei, UNISFA, na kokarin shawo kan rikicin kabilanci tare da samar da kayan agaji amma ke fuskantar cikas saboda cijewar tattaunawa tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu a cewar jakada Robert Wood, wakilin Amurka a kan harkokin siyasa a MDD.
“A kasar Sudan, rikici ya jefa aikin UNISFA a cikin hatsari tare da hanata damar sauke nauyin da aka dora mata, ciki har da bada kariya ga fararen hula, da samar da kayayyakin agaji da kuma taimakawa wajen fayyace matsayar Abyei ta karshe cikin lumana da batutuwan da suka shafi kan iyokin yankin, tare da kafa rundunar ‘yan sandan Abyei.”
Jakada Wood ya jaddada takaicinsa na rashin samun wani muhimmin ci gaba game da batun fayyace makomar yankin Abyei ta karshe, daga jerin batutuwan da har yanzu ba’a cimma matsaya a kansu ba. A irin wannan yanayi, rikicin kabilanci na ci gaba da zama barazana ga fararen hula a kudancin Abyei, a cewar jakada Wood
Amurka ta yi matukar damuwa da milyoyin farar hula dake da bukatar muhimman kayayyakin agaji a suda sannan tayi allawadai da kowane irin hare akan ma’aikatan bada agaji dake yankin, a cewar jakada Wood:
“Amurka na kara nanata kiranta ga dukkanin bangarorin dake cikin rikicin dasu mutunta aminci da tsaron ilahirin jami’an mdd da jami’an bada agaji dana kiwon lafiya.
Muna matukar bukatar dukkanin bangarorin dasu tabbatar UNISFA da jami’an bada agajin sun gaggauta samun cikakkiyar dama mara hatsari ta shiga lungu da sako na Abyei domin gudanar da ayyukansu masu muhimmanci sannan Sudan da Sudan ta Kudu su bari a samu zirga-zirga cikin ‘yanci (domin aikin tantancewa da kula da kan iyaka na hadin gwiwa) ya aiwatar da kudirin da aka dora masa.”
“Muna ci gaba da nuna goyon baya ga al’ummar sudan a fafutukar ta kafa tsarin dimokiradiya,” a cewar jakada Wood,” sannan muna kira ga (rundunar mayakan sudan) da (kungiyar ‘yan tawayen RSF) su aiwatar tare da kiyaye tsagaita wuta ta dindindin a fadin kasar.”
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.