Shahararran Mawakin Najeriya Burna Boy Ya Lashe Kyautar Grammy

Shaharraren mawakin nan Damini Ebunoluwa Ogulu da aka fi sani da Burna Boy ya sami lambar yabo ta wakar da ta fi fice a duniya bana a babban taron fidda gwani na fitattun mawakan duniya da ake kira Grammy.

An saba gudanar da bukin karrama mawakan da su ka yi fice a duniya da ake kira Grammy Awards, kowacce shekara a Amurka, inda jiga-jigan kade-kade da raye-raye ke taruwa a birnin Los Angeles na Amurka a karshen watan Janairu, amma aka ɗage zuwa watan Maris saboda karuwar cutar coronavirus.

Grammys da aka gina a akan wasanni, ya hada da raira waƙoƙi, kuma tare da babban taron domin bada lambar yabo ga mawaka.

Masu shirya taron a bana sun dauki matakai na ban mamaki don bada kariya ga wadanda suka je da kuma masu yada labarai. An tabbatar da cewa kafofin watsa labarai da aka gayyata ciki yayin shirye-shiryen, suna yin gwajin COVID-19 akai-akai.

Ana kashe miliyoyin dalar Amurka makudan wajen shirya bukin karrama fitattun makawan, kuma mawaka sukan cashe su sheke ayarsu, amma COVID-19 ta sauya tsarin na wannan shekarar.

A wannan shekarar an karrama mawaka kamar su Beyoncé, Megan Thee Stallion, John Legend da kuma Burna Boy shahararran mawaki daga Najeriya.

Beyoncé

Burna Boy ya lashe kyautar Kundin Wakokin Duniya na Duniya saboda sabon aikinsa na karshe, ‘Twice As Tall’ inda a wannan bangaren ya doke Ba'amurke, rukunin ƙungiyar wasan kwaikwayo ta Antibalas da ke Brooklyn; kungiyar mawakan Abzinawa, Tinariwen; Mawakiyar Burtaniya ‘yar asalin Indiya, Anoushka Shankar da mawakiya ’yar asalin Brazil Ba'amurkiyar, Bebel Gilberto.

’Yan Afirka da musamman ‘yan Najeriya sun nuna farin cikinsu da kyautar Grammy da Burna Boy samu kuma nan take shafuffukan sada zumunta suka fara yadawa suna taya shi murna.

Tauraron Burna Boy wanda ya ke daya daga cikin fitattun mawaka da raye raye da kuma maruba wakoki a nahiyar Afrika, ya fara haskawa ne a shekara ta 2012 lokacin da ya fitar da wata waka da ake kira "Like to Party" daya daga cikin jerin wakokin da ke cikin wakokin sa na farko da ya fitar a dunkule.

A shekara ta 2017, Burna Boy ya sa hannu a yarjejeniyar kwangilar wake wake da kamfanin harhada wakoki da ake kira Bad Habit Atlantic Record na Amurka.

Ya sami lambar yabo ta fitattun mawaka bakaken fata "BET AWARDS" a shekara ta 2019. Ya kuma sami lambar yabo ta makawakan Afrika da suka fi fice a bukin yaba fitattun makwa na VGMA a shekara ta 2020.

An haifi Burno Boy, dan shekaru 29, ranar 2 Juli, 1991 a garin Patakwal na jihar Ribas. Ya kuma yi kaurin suna tsakanin mawakan Najeriya da kuma sauran kasashen nahiyar Afrika sabili da yawan fadan ra'ayinsu kan batutuwa masu sarkakiya.