Shafin Neman Rancen Karatun Dalibai Zai Fara Aiki A Ranar 24 Ga Watan Mayu

Dalibai Na Rubuta Jarabawar JAMB A Najeriya

A cewar NELFUND, dalibai zasu neman rance domin cimma burinsu na karatu ba tare da wata matsala ba.

A jiya Alhamis, Hukumar Kula da Asusun Bada Rancen Karatu ta Najeriya (NELFUND) tace za’a bude ashafin neman rancen karatun a ranar 24 ga watan Mayun da muke ciki.

"An tsara shafin ta yadda dalibai zasu mika bukatunsu na neman rancen karatun cikin sauki da nisahdi.

"Muna karfafa gwiwar duk daliban da suka cancanta dasu ci gajiyar wannan dama ta zuba jari a rayuwar gobensu tare da bada tasu gudunmowa wajen bunkasar kasarmu.

"Daliban zasu samun shiga shafin ta adireshin yanar gizo na http://nelf.gov.ng domin fara mika bukatar neman rancen karatun" a cewar wata sanara da NELFUND ya fitar.

A watan Yunin daya gabata ne, Shugaba Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin dokar rancen daliban, domin tallafawa daliban Najeriya dake karatu a manyan makarantu.

An amince da dokar ne bayan zaman nazari daban-daban da kwamitocin zaurukan majalisun tarayya 2 akan ilmi da NELFUND suka yi.

An nada Mr. Akintunde Sawyer a matsayin Babban Darakta kuma Shugaban Asusun na NELFUND a yayin da aka nada Mr. Fredrick Oluwa Femi Akinfala a matsayin Daraktan Harkokin Kudi da Mulki da Mustapha Iyal a matsayin Daraktan Ayyuka.

Daga bisani Shugaba Tinubu ya nada Mr. Jim Ovia a matsayin Shugaban Hukumar Daraktocin Asusun na NELFUND a ranar 26 da watan Afrilun daya gabata.