Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kirkiro Manhajar Tsarin Rancen Dalibai


Gwamnatin Najeriya ta ce za ta samar da manhajar tsarin rancen kudin dalibai

Hakan ya fito ne a cewar Babban Sakataren Hukumar Kula da Rancen dalibai, Akintunde Sawyer wanda yayi magana a ranar Litinin bayan da hukumar ta gana da Shugaban Kasa Bola Tinubu a Abuja.

Sawyer ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa an cire duk wani shishshigi da katsalandan na mutane cikin harkokin tafiyar da tsarin wanda ake da shirin farawa a wannan shekara

Wannan ci gaban ya zo ne watanni bayan Shugaba Tinubu ya ce shirin zai fara ne a watan Janairun 2024.

"A watan Janairu 2024, sabon tsarin lamunin dalibai dole ne ya fara. A nan gaba kadan muna masu tabbatarwa da yakinin cewa ‘ya’yanmu da dalibanmu albishir na babu sauran yajin aiki,” in ji Tinubu a Abuja yayin taron tattalin arzikin kasa na 2023, inda ya tabbatar wa daliban cewa zamanin yajin aikin ya wuce.

Shugaba Tinubu a bikin ranar 12 ga watan Yuni, ranar dimokradiyyar Najeriya, ya rattaba hannu kan kudirin ba da lamuni na dalibai domin cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa.

Kudirin dokar wanda Shugaban Majalisar Wakilai ta 9 Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya dauki nauyinsa, ya samar da sauki ga ‘yan Najeriya masu karamin karfi wajen samun guraben manyan makarantu ta hanyar lamuni mara kudin ruwa daga asusun bayar da lamuni na ilimi na Najeriya.

Kudaden shirin zai kasance a cikin ma’aikatar ilimi kuma daliban da ba su da karfi na manyan makarantu za su samu damar shiga.

~Yusuf Aminu Yusuf ~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG