Sergio Aguero Ya Kafa Tarihi A Manchester City

Sergio Aguero

Shahararen dan wasan gaba na Kasar Argentina, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, mai suna Sergio Aguero, ya kafa tarihi a kungiyar Manchester City, dan wasan ya kasance dan wasan da yafi kowani dan wasan Manchester City zurara kwallaye a raga a kungiyar.

Aguero mai shekaru 29, da haihuwa, ya samu nasarar shiga tarihin ne a wasan da kungiyarsa ta Manchester City, tayi tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Napoli, na Kasar Italiya, ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a wasan rukuni inda ta doke Napoli daci 4-2 a Italiya.

Dan wasan shi ya jefa kwallo na uku a cikin kwallaye hudun bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a mintuna na 69, hakan ya sa Aguero ya cika jimilar kwallaye 178, a wasannin daban daban da ya buga wa kungiyar ta Manchester City, tun zuwansa kungiyar a shekarar 2011 daga Atletico Madrid.

Sergio Aguero ya karbi wannan kambun ne daga hanun tsohon dan wasan Manchester City mai suna Eric Brook, wanda ya Zurara kwallaye 176, a cikin wasanni 528, da ya buga a kungiyar tun shekara 1928-1936 kimanin shekaru sama da tamanin da suka wuce.

Your browser doesn’t support HTML5

Sergio Aguero Ya Kafa Tarihi A Manchester City - 5'48"