‘Yan kungiyar ISIS sun dauki alhakin kai harin a wani birni na Kuwait, biyo bayan hare-hare guda biyu makamantasu da aka kai kan masallacin ‘yan shi’a a Saudi cikin watan Mayun da ya gabata wanda shi ma ‘yan ISIS din suka dauki alhakin kai shi.
Yau Talata, Kamfanin dillacin labaran Saudi mallakar gwamnati, ya ambaci wani jami’in ma’aikatar cikin gida yana cewa, an kame daya daga cikin mutanen a Kuwait, na biyun kuma yana hannu yanzu haka a birnin Taif dake kudu maso yammacin Saudi. An kuma tsare mutum na 3 a kusa da iyakar Saudi da Kuwait bayan wata musayar wuta da suka yi wadda har jami’an tsaron Saudi 2 sun jikkata.
Mutum na hudu kuma yana can yana fada tare da ‘yan kungiyar ISIS a Syriya, a cewar ma’aikatar.
‘Yan kungiyar ta ISIS masu tsattsauran ra’ayi suna daukar ‘yan shi’a tamkar ba musulmai ba kuma sun sha auna su a hare-hare a wannan yankin.