Bayanai da ga rundunar soja, sun nuna tun ranar da aka sace marigayin aka yi masa kisan gilla, mutane dai sun saba bayar da diyya a sako yan uwansu idan irin wannan lamarin ya faru da gwamnati ko jami’an tsaro ke cewa gurguwar dabarace dake sa masu satar kara bullo da dabaru da ci gaba da sace jama’a don neman kudi ta haramtacciyar hanya.
Inba a manta ba tsohon dan majalisar jihar Gwambe Jalo Gangama, an taba sace shi wajen sallar Asuba, inda masu satar suka taryar da sahun sallah tare da shi. Kafin daga bisani Allah ya kubutar dashi.
Haka nan shima mai fina finan Nollywood Kidochi, yace matasan da suka sace shi sunyi ta yi masa hidima koda za a ce irin wannan hidimar ta kan juye zuwa hannun jarin samun kudin fansa mai tsoka.
Imran Hassan mai nazari ne kan harkokin yau da kullum, wanda yasan rikicin Sudan da sauran lamurra na laifukan yankin Afirka a jam’iya da Arabiya ya raba ajin masu sace mutane har kashi uku. Inda yace akwai masu sace mutane saboda harkar tsafe tsafe, wanda ke sace mutane domin cire musa wasu sassa na jiki. Akwai kuma masu satar manya domin neman kudin fansa da kuma masu satar mutane domin suyi kisa.
Anasa bangaren kwararre kan harkar tsaro Kabiru Adamu, na ganin ya zama wajibi jami’ai su ke rinka amfani da fasahar zamani wajen magance wannan matsalar. inda yace masu satar mutane na amfani da wayar wanda suka sace saboda suna ganin idan sukayi amfani da wayarsu ana iya gano su, kasancewar yan sanda sunyi ta karbar kudi don su sayo na’urar da zata tabbatar musu inda ake waya. Idan kuma jami’an basa amfani da wannan na’urar to sai su fito suyi bayani.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5