Satar Fasaha Ba Shine Babban Kalubalen Kannywood Ba

Hafiz Bello Kannywood

A yau Shirin mu na nishadi na mussamam ne domin kuwa mun sami zantawa da darakta Hafiz Bello, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda aka karama a kwanakin baya a kasar Ingila domin rawar da yake takawa a faggen fina finai.

Hafiz Bello ya ce ya samu award har guda uku da fim dinsa na Bincike a shekara ta 2015.

Fim din Bincike fim ne da ya kunshe labarin wani dan sanda da ya kashe matarsa aka kuma zo bincike daga bisani aka gano shi ya kashe matar tasa.

Darakata ya ce ya fara harkar fim tun 1998 inda ya fara harkar da mai rike micro phone ya koyi rike kamara daga bisani ya tsinci kansa a matsayin darakta.

Darakta Hafiz ya ce kalubalen da suke fuskanta dai bai wuce rashin wayerwar kai a harka fim ba , a cewarsa bai yarda satar fasaha ne babban kalubalen Kannywood ba illa dai rashin wayewar harkar ta fim da tsare-tsaren da ya kamata.

Hafiz Bello ya ce fim da ya fi burgeshi har kawo yanzu bai fito ba shekara goma kenan da kammalla wannan fim mai suna WAKIYA … ku biyo mu domin jin ko me ya hana fim din fitowa har kawo yanzu.