An samu yara ‘yan misalin shekara goma sha biyar 15, masu fasaha da suka fito da muhiman hanyoyi na ci gaban kimiyya a wannan shekarar. A kowace shekara, akwai gasar gwajin kwakwalwa da ta danganci lisafi, ayukkan kimmiya, fasahar na’ura, da kere-kere a gun matasa domin a zabi mutun biyu don basu kyautar kudi dala dubu asharin $20,000 dai-dai da naira 5,000,000 wanda yazo na daya.
Wanda yazo na biyu kuma dala dubu goma $10,000. Sannan a zabi dalibai ashirin da takwas domin karramasu akan aikin gwaninta da sukayi. Wannan daliban guda talatin sunyi gwagwarmaya da dalibai da dama a kasashe kafin samun nasarar wannan gasar ta “Broadcom MASTERS” da akayi a karshen wannan shekarar.
Daga cikin daliban akwai, Andrew Eggebraaten, mai shekara goma sha hudu 14, wanda ya kera hannun karfe mai umfani da na’ura. A shekarun Andrew, ya zama gwani wurin aiki da lantarki domin sarrafa abubuwan al’ajabi. Wannan hannun mai amfani da na’ura yana gudanarda ayuka daban-daban har kashi hamsin da takwas 58%. Abun karin ban sha’awa shine ana iya bashi ummurni ta hanyar yin magana domin ya gudanar da aikin.