A shirin samartaka na wannan makon, dandalin voa ya sami zantawa ne da wasu matasa samari da 'yan mata, wadanda suka bayyana ra'ayoyin su dangane da dalilan da ke sa 'yan mata kanan da dama bin maza musamman magindanta, wadanda za su iya kasancewa sun girmi iyayen su.
Mun fara jin ta bakin 'Yan matan ne inda wasu suka nuna cewa hakan na faruwa ne saboda wasu dalilai da suka hada da kula, wato idan namiji ya kai wasu shekaru ya fi tsayawa ya kula da budurwa fiye da matashi.
Wasu kuma sun nuna cewar kwadayin abin duniya ne ke kai su, koda shike ba'a taru an zama daya ba, amma mafi yawanci hangen abin duniya ne ke kai su a cewar wasu daga cikin 'yan matan.
Daga karshe wasu daga cikin 'yan matan sun bayyana cewar su dai baza su iya nema da duk wanda ya girme su da shekaru sama da goma ba, koda shike wani lokaci sukan yi maneji domin su rika samun 'ya'yan banki suna toshe wata kafar mai makon dogara ga iyaye ko samari matasa sa'o insu.
Saurari cikakkiyar hirar a dandalinvoa.com