Sata na kan gaba a zaben Shugaban kasar Zambia

  • Ibrahim Garba

Mr. Michael Sata kenan tare da magoya bayansa

Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Zambia na nuna cewa

Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Zambia na nuna cewa babban mai kalubalantar Shugaba mai ci Mr. Michael Sata, ya sha gaban Shugaba mai ci din wato Rupiah Banda.

Hukumar Zaben Zambia ta fadi a yau Laraba cewa kodayake ana kan kidaya kuri’un, Mr. Satan a jam’iyyar Patriotic Front ya ci kashe 42 % na kuri’un da aka kada. Mr. Banda na Movement for Multiparty Democracy ne ya zo na biyu da kashi 35%.

Hakainde Hichilema na jam’iyyar UPND shi ne ya zo na uku da kashi 18%.

Hukumar zaben ta ce an sami wadannan alkaluman ne daga mazabu 133 daga cikin mazabu 150.

Binciken jin ra’ayin jama’a ya nuna za a yi kare-jini biri-jini tsakanin Shugaba banda da Mr. Sata, wanda ke yin takarar shugaban kasa a karo na hudu kenan.

An sami rahotannin tashe-tashen hankula nan da can a jiya Talata a babban birnin kasar, wato Lusaka, to amman masu sa ido na Tarayyar Turai sun ce an gudanar da zaben ta hanyar da ta dace. Shugabar tawagar Turai na sa ido Maria Muniz ta bayyana zaben da cewa mai inganci ne.