Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Michael Sata A Zaman Shugaban Kasar Zambiya


Ana rantsar da sabon shugaban Zambiya, Michael Sata, a farfajiyar kotun kolin kasar dake Lusaka, yau Jumma'a 23 Satumba 2011.
Ana rantsar da sabon shugaban Zambiya, Michael Sata, a farfajiyar kotun kolin kasar dake Lusaka, yau Jumma'a 23 Satumba 2011.

Kasa da kwana guda bayan da aka ce dadadden shugaban hamayyar ya lashe zaben shugaban kasa, an rantsar da shi a kan wannan mukami a Lusaka

An rantsar da dadadden shugaban hamayya na kasar Zambiya, Michael Sata, a zaman shugaban kasa, abinda ya zamo maida mulki daga wannan gwamnati zuwa wancan ta hanyar dimokuradiyya a karo na biyu a kasar tun samun 'yancinta daga kasar Ingila.

A yau Jumma'a hukumar zabe ta bayar da sanarwar cewa Sata, mai shekaru 74 da haihuwa, kuma mai farin jini a wurin jama'a, ya doke shugaba mai ci, Rupiah Banda, a wannan zabe na shugaban kasa.

A taron 'yan jarida da yayi da kwalla a idanu, shugaba Banda ya yarda an kayar da shi, yana mai fadin cewa, "Al'ummar Zambiya sun yi hukumci, kuma tilas mu yi aiki da hukumcin nasu." Ya roki magoya bayansa da kada su yarda su nemi tayar da fitina, yana mai cewa yanzu ba lokaci ne na tashin hankali ba.

Magoya bayan Mr. Sata sun bazu kan tituna su na murna a bayan da hukumar zabe ta ayyana sakamakon zaben jim kadan bayan karfe sha biyun dare agogon kasar.

XS
SM
MD
LG