Sarakunan dai sun hadu ne a wajen taron taya sarkin Ningi na 16, Alhaji Yunusa Danyaya, murnar cika shekaru 40 kan karagar masarautar Ningi.
Mai alfarma sarkin Musulmi ya bai wa al’umma shawarar cewa ganin yadda lokacin zabe ya karato, kada wanda ya bari shugabannin siyasa su yi amfani da kudi wajen jefa su wata harka da ba ta kwarai ba.
Haka kuma mai alfarman ya yi kira ga kowa ya je ya yi rijistar zabe domin yin amfani da ita wajen zaben shugabannin da suka dace.
A nashi jawabin mai martaba sarkin Kano, ya yabawa shugabannin siyasa da suke martaba masarautun gargajiya, don mutunta tarihi da kuma hadin kai don taimakawa al’umma.
Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, uban taro mai martaba Alhaji Muhammadu Yunusa Dan Yaya, ya yi tsokaci ne kan matsayar masarautun gargaji a tsarin mulkin kasa.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5