Sarki Sanusi Na Biyu Da Lamido Muhammad Barkindo Sun Gana Da Fulani Makiyaya

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi na Biyu, da mai martaba Lamidon Adamawa, Muhammad Barkindo Aliyu Mustafa, sun gana da kungiyoyin Fulani makiyaya a Minna ta Jihar neja, a wani yunkurin shawo kan rikice-rikicen dake faruwa masu alaka da kiwon shanu.

Wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, ya ambaci shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru, yace daga cikin matsalolin da suka tattauna da sarakunan har da batun samar da burtalolin shanu da kuma abubuwan da suke faruwa a jihohin Binuwai da Taraba, inda gwamnoninsu suka kafa dokoki na hana Fulani yin kiwo.

Ardon Zuru yace ummul haba'isin wannan fitina ita ce wadannan dokokin da jihohin suka kafa wadanda suka saba da dokokin kasa a Najeriya.

A jawabinsa a gaban al'ummar Fulani makiyayan, mai martaba Sarki Sanusi ya roke su da su kasance masu hadin nkai a tsakaninsu, yana mai cewa "duk sadda aka ce ku zo taro a Abuja, to ku sanar da mu."

Sarkin yace yin hakan, zai ba sarakunan sukunin tabbatar da cewa makiyayan sun samu wakilan da zasu iya kare muradunsu a wurin duk wani taron da za a yi, yana mai misali da yadda shugabannin Binuwai masu adawar siyasa da juna suka hadu suka je wurin taro a lokacin da aka kira su don tattauna tsaro.

Sarki Sanusi yace ya zamo tilas ga su ma al'ummar Fulani su rika zuwa irin wannan taron da mutanen da zasu iya yin magana a madadinsu, daidai da wadanda suke zuwa su na magana a madadin sauran mutanen da suke takaddama da su.

Mustapha Nasiru Batsari yace bayanai sun nuna cewa wannan shine karon farko da manyan sarakunan Arewa suka kira irin wannan taron da ya hado kan dukkan kungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriya domin tattauna abubuwan dake damunsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kano Da Lamidon Adamawa Sun Gana Da Fulani Makiyaya A Neja - 2'58"