Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kabilu Daga Numan Da Demsa Sun Kai Hari Kan Fulani A Shelleng


Rikicin makiyaya da 'yan kabilar Bachama a jihar Adamawa
Rikicin makiyaya da 'yan kabilar Bachama a jihar Adamawa

A maraicen Asabar ne aka kai harin kan yankin na Libbo dake karamar hukumar Shelleng.

Kamar yadda rahotanni ke cewa an samu hasarar rayuka da dama na Fulani makiyaya a yankin Libbo dake karamar hukumar Shelleng, bayan da wasu kabilu daga kananan hukumomin Demsa da Numan suka kai musu hari dake kama da na ramuwar gayya.

Kamar yadda bayanai ke cewa, baya ga asarar rayuka, an kona gidaje da kuma dabbobi,kuma wannan tashin hankalin ya samo asali ne bayan da aka tsinci gawar wani mutum na al’umman Gomba dake karamar hukumar Demsa, inda ake zargin cewa wasu Fulani ne suka kashe shi.

Da yake tabbatar da aukuwar wannan tashin hankali,Hon. Shuaibu Waleed, kansila dake wakiltar yankin Libbo, yace tuni aka tura jami’an aro don maido da doka da oda.

Shima dai da yake tabbatar da wannan sabon hari kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa SP.Othman Abubakar yace an tura wani rukunin yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin don zakulo wadanda ke da hannu a wannan hari tare da maido da doka da oda.

Kakakin yan sandan a sakon kar ta kwanan da ya aike min, ya bukaci jama’a da suke sa ido, da kuma kaucewa daukar doka a hannu.

Wannan dai na ko zuwa ne yayin da Gwamnan jihar Adamawa Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla wanda ya nuna damuwarsa game da tashe tashen hankulan dake aukuwa cikin kwanakin nan yace,dole ayi karatun ta natsu,musamman a wannan lokaci da jihar ke zawarcin masu son zuba jari a jihar.

Wasu dai na danganta irin tashe tashen hankulan dake faruwa ayanzu da adawar siyasa. Alh.Suleiman Muhammad Jada,yace bai kamata abun dake faruwa a jihar Adamawa yake faruwa ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG