Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Nan 10 Da Boko Haram Ta Sako Ba 'Yan Sanda Ba Ne


Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Borno, Damian Chukwu
Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Borno, Damian Chukwu

Hukumomin 'yan sanda a Jihar Borno sun sake nanata matsayinsu na cewa matan da Boko Haram ta sako daga cikin wasu mata 16 da ta kama ba jami'an 'yan sanda ba ne, haka kuma ba su auren wani dan sanda kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka yi ta yayatawa.

A karshen makon nan ne gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar cewa an sako wasu mutane 13 da Boko Haram ta kama ta yi garkuwa da su, cikinsu har da malaman jami'ar Maiduguri su uku da aka kama cikin watan Yuli, da kuma mata 10 daga cikin wadanda aka kama a kan hanyarsu ta zuwa Lassa domin halartar jana'izar wata 'yar sanda da ta rasu.

Sai dai kuma, kwamishinan 'yan sanda na Jihar Borno, Mr. Damian Chukwu, ya ce lallai daga cikin matan da aka kama su a kan hanyar zuwa Lassa din a wancan karon, akwai wata 'yar sanda guda daya mai mukamin sufeto, wadda kawa ce ta 'yar sandar da ta rasu, kuma tana cikin masu zuwa ta'aziyya da jana'izar.

Mr. Chukwu ya yaba ma wasu 'yan sandan da suka harbe suka kashe wasu mata 'yan kunar-bakin-waken da suka yi kokarin kutsawa cikin ofishin 'yan sanda na garin Dikwa a watan da ya shige, yana mai cewa sun ceci rayukan jama'a domin in ban da 'yan kunar-bakin-waken babu wanda ya mutu.

Haka kuma yace jami'an 'yan sanda karkashin jagorancin DPO na garin Magumeri, sun kai dauki ma wasu Fulani makiyaya da 'yan Boko Haram suka sace tare da shanunsu, inda suka samu nasarar kubutar da wadannan mutane da dukkan dabbobinsu. Haka kuma sun samu ganimar makamai da dama daga hannun mayakan Boko Haram din da suka gudu.

Kwamishinan 'yan sanda na Jihar ta Borno, Mr. Chukwu, yace wata babbar matsala ko masifa dake karuwa a Jihar ita ce fyade ma yara mata kanana, inda yace akan samu masu shekaru 50 zuwa sittin da haihuwa suna fyade ma yaran da ba su wuce shekaru 4 zuwa 12 ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG