Sarki Charles III Na Fama Da Cutar Kansa

Sarki Charles III

A jiya litinin masarautar Buckingham ta bayyana cewa, Sarki Charles na 3 ya kamu da cutar sankara kuma tuni ya fara karbar magani, duk da dai masarautar bata bayyana ko wacce irin sankara  sabon Sarkin Ingilan ya kamu da ita ba.

Kasa da watanni 18 da hawa gadon sarautar, Sarki Charles mai shekaru 75 a duniya zai dakatar da ayyukan masarautar na dan lokaci, amma zai cigaba da gabatar da ayyukan da suka shafi kasa, kuma ba zai dakatar da ayyukan da tsarin mulki ya dora ma shi ba, a cewar wata sanarwa da masarautar ta Buckingham ta fitar.

Batun cutar kansar ya bayyana ne bayan da Sarki Charles ya shafe kwanaki 3 a asibiti a watan jiya, sakamakon wata yar karamar tiyata da aka yi ma shi.

Masarautar ta kara da cewa, tun a lokacin kwanciyar ta shi a asibitin ne aka lura da wata matsalar a kwance, amma dai ba a bayar da wani karin bayani ba, illa dai cewa, gwaji ya nuna Sarkin na da wani nau’in cutar kansa a tare da shi.

Charles ya zama Sarki ne a watan Satumba na 2022 bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, wadda ta rasu tana da shekaru 96 bayan ta shafe shekaru 70 akan karagar mulki.

Labarin cutar na zuwa ne yayin da surukarsa Kate, Gimbiyar Wales, ta ke murmurewa daga tiyatar da ta yi mata a asibiti kusan makonni biyu da suka gabata.