Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jill Biden Na Halartar Bikin Nada Sarki Charles III A London


Jill Biden a hannun hagu tare da matar Firaministan Birtaniya, tsakiya
Jill Biden a hannun hagu tare da matar Firaministan Birtaniya, tsakiya

Babu wani shugaban Amurk da ya taba halartar bikin nadin sarauta a Birtaniya.

Uwargidan shugaban Amurka Jill Biden na daya daga cikin manyan bakin da aka gayyata wajen bikin nadin sarautar Sarki Charles na UKU.

Shugaba Biden ne ya tura mai dakinsa, don ta wakilci Amurka a nadin sarautar wacce za a yi a yau Asabar.

Babu wani shugaban Amurk da ya taba halartar bikin nadin sarauta a Birtaniya.

Bayanai sun yi nuni da cewa Jill Biden ta kwashe yinin jiya tare da Akshata Murty, uwargidan Firai Ministan Birtaniya Rishi Sunak.

A ranar Lahadi ake sa ran za ta koma Washington.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG