Daruruwan dubban mutane ne suka yi jeru a titunan birnin London a ranar Asabar, don shaida bikin nadin sarautar Sarki Charles III, bikin da aka baje al’adu iri-iri da miliyoyin mutane suka kalla ta talbijin da kafar intanet a sssan duniya.
Shugabannin kasashe, sarakun da sarauniyoyi 90 daga sassan duniya suka halarci bikin wanda aka yi a Westminster Abbey.
Fadar Buckingham ta ce kasashe 203 ne suka tura wakilai a bikin na nada Sarki Charles mai shekaru 74, wanda tun yana shekaru uku da haihu ya zama yarima mai jiran gado, a lokacin da mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II ta hau karagar mulki.
A ranar 8 ga watan Satumbar bara Charles ya dane karagar mulki bayan rasuwar mahaifiyar tasa.
Wani keken gwal mai dadadden tarihi ya dauki Sarki Charles III da Sarauniya Camilla daga Fadar Buckingham zuwa Westminster da safiyar ranar ta Asabar.
Duk da ruwa da aka yi ta yi, daruruwan mutane sun yi jerin gwano a hanyar da Sarkin zai wuce, daidai da yadda suka yi watanni takwas da suka gabata a lokacin jana’izar Sarauniya Elizabeth II.