Sarakunan Gargajiya A Jihar Adamawa Sun Bukaci Hukumar Zabe Ta Kara Azama

Sarakunan gargajiya sun yi fadakarwa a jihar Adamawa, yayin da hukumar zaben Najeriya INEC, ke kara wa’adin sabunta katin zabe watau Voters Card domin fuskantar zabuka masu zuwa.

To sai dai kuma duk da wannan wa’adin da aka kara a jihar Adamawa, da alamun akwai wasu al’ummun dake jan kafa wajen sabunta katin zaben batun da yasa yanzu sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki yunkurowa.

ko wane irin gargadi ne sarakunan ke yiwa irin wadannan al’ummu? Alhaji Muhammadu Inuwa Baba Paris, Dan Isan Adamawa kuma hakimin Jimeta, dake zama cibiyar mulkin jihar yace lamidon Adamawa Dokta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa shine ya umurce su, da su tashi haikan wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin katin zaben, inda yace yanzu haka suna bukatar Karin cibiyoyin karbar katunan.

Baya ga batun sabunta katin zaben, wani batu da yanzu haka ke gaban hukumar zabe INEC, a jihar shine na batun karancin runfuna da akwatunan zabe musamman a yankunan da kawo yanzu basu da wuraren kada kuri’a.

Hon.Usman Kaura, wani dan jam’iyar PDP a jihar wanda ya bayyana halin da ake ciki game da wannan matsalar, yace lokaci yayi da za’a kara runfuna da kuma wuraren kada kuri’a a jihar.

Sai dai ko a nata bangaren, hukumar zaben INEC, ta sha alwashin duba wannan batu. Barrister Kassim Gana Gaidam, dake zama kwamishinan zabe a jihar yace suna sane da matsalar kana kuma yace aikin sabunta katin zabe na tafiya babu kama hannun yaro.

Ga rahoton Ibrahim Abdul’aziz domin cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarakunan Gargajiya A Jihar Adamawa Sun Bukaci Hukumar Zabe Ta Kara Azama