Rundunar ‘yan Sandan Najeriya, ta sake musanta sabon zargin da Sanata Isa Hamma Misau, ya sake yi dake nuna babban Sufeton ‘yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya baiwa uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, kyautar motocin alfarma biyu.
Jami’in labarun rundunar Moshood Jimoh, yace an tura motocin biyu ne domin aiki tsaro ga kwambar motocin uwargidan shugaban bisa bukatar haka daga dogarinta Sani N. Baba.
Haka kuma rundunar ta sake musanta wani zargin na Isa Hamma, dake cewa babban Sufeton ya bada bayanai da ba dai daiba kan yawan shekarunsa a takardunsa na aikin Dan Sanda, Jimoh, yace wani kuskure kawai aka gyara na banbancin kwanaki goma sha biyu a kwanan watan da aka haifi Sufeton a 1959.
Sanata Isa Hamma Misau, ya sake nanata zargin nasa yana mai cewa sun duba sun gani ranar da yakamata shi Sufeton Dan Sandan ya yi ritaya ranar 3, ga watan daya shekarar 2019, amma sai gashi yanzu an canja shi zuwa 15, ga watan daya 2019.
Bala Ibrahim, mai taimakawa babban Sufeton ta fuskar labarum yace gaskiya zatayi halinta, domin gwamnatin tarayya ta riga ta shigar da kara domin Isa hamma Misau, yaje ya tantance zarge zarge da ya yiwa Sufeto janar na ‘yan Sanda.
Ya kuma kara da cewa majalisa itama ta kafa kwamiti kuma ana san ran cewa zasuyi aiki mai kyau.
Wannan dambarwar dai tana gaban kotu, kamar yadda ofishin Ministan shara’a Abubakar Malami ya shigar da karar Sanata Misau a madadin gwamnatin Najeriya.
Facebook Forum