Yanzu haka gwamnatin jihar Kaduna ta fara daukan sababbin ma’aikata, kamar yadda ta alkawarta a kwanakin da suka gabata cewa zata dauki mutane dubu ashirin da biyar.
Malam Samuel Aruwan, shine mai Magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, ya ce suna wannan abu ne da kyakkyawar manufa, ya kara da cewa gwamnatin jihar ta fitar da tsarin jaddawalin daukan malaman makaranta, duk wanda ya mallaki irin takardun, wannan dama ta bude domin su, kuma za a ci gaba da amsar takardun har zuwa tara ga watan Nuwambar wannan shekara.
Da yake amsa tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Isa Lawal Ikara, ya yi masa, Mr Aruwan, ya bayyana cewa bashi da masaniyakan yajin aikin ada kungiyar malaman tace zata tafi.
Shugaban kungiyar malam da sakataren shi sun ce sun riga sun kammala bada bayanai ga manema labarai, sun kara da cewa yanzu haka ma sun garzaya birnin tarayya Abuja, domin su bayyanawa uwar kungiyar matakin da suka dauka a jihar Kaduna.
Sai dai kuma wani mai fashin baki kuma lauya mai zaman kanshi Barista El-Zubair Abubakar, ya ce wannan lamari na korar malaman makaranta na bukatar idan an bugi jaki to lallai a bigi Taiki.
Domin karin bayani, saurari rahoton Isa Lawal Ikara.
Facebook Forum