Sarakuna Da Malamai Sun Fara Magana Kan Kuncin Rayuwa A Najeriya

Masu zanga-zanga rike da alluna dake dauke da sakonni ga gwamnatin Najeriya.

Kuncin rayuwa da talakawan Najeriya ke ci gaba da fuskanta ya sa Sarakuna da Malaman addinai sun fara fitowa karara suna jan hankalin shugabannin kasar, amma fadar shugaban Najeriyar tace tana sane.

Yan Najeriya ba zasu taba mantawa da yadda shahararren Malamin addinin Kristan nan Rev Father Mbaka, yayiwa gwamnatin Goodluck Jonathan wankin babban bargo ba. A yan kwanakin nan sai da mai Martaba Sarkin Kano Mallam Mahammadu Sunusi na biyu, yaja hankalin gwamnatin tarayya dangane da yadda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da tabarbarewa.

Shima shahararren malamin addinin musuluncin nan da ke da karfin fada aji tsakanin musulman kasar, Shiek Dakta Ahmed Mohammed Bamba Yabara, yayi kira da lalle a samarwa da al’umma abinci kada a barta cikin yunwa, domin gujewa tambayar ubangiji ranar hisabi.

A mayar da martanin gwamnati kakakin fadar gwamnatin kasar Mallam Garba Shehu, yace gwamnati na sane kuma idan aka duba kasafin kudin bana da gwamnatin tarayya tayi akwai wani kaso na musamman har Naira Biliyan Dari Biyar, domin a taimakawa masara karfi a Najeriya, wanda ba a taba yin irinsa ba.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarakuna Da Malamai Sun Fara Magana Kan Kuncin Rayuwa A Najeriya - 2'24"