Akan furucin da sarkin Kano Sanusi II yayi game da tattalin arzikin Najeriya Muryar Amurka ta tuntubi gwamnatin tarayya da masana tattalin arziki da ma wasu mutane domin jin ra'ayoyinsu.
Kakakin fadar shugaban kasa, Malam Garba Shehu yace gwamnatin Buhari gwamnati ce ta dimokradiya da kuma jama'a. Yace saboda haka kullum a shirye take ta saurari shawarar jama'a. Yace ba kuskure ba ne mutum yace gyara kayanka. Babu inda ake gwamnati tace ta san komi dari bisa dari. Dole ta saurari jama'a idan akwai bukatar gyara sai a yi.
Yushau Aliyu kwararre akan harkokin tattalin arziki yace tsakanin babban bankin Najeriya da shugaban Najeriya an samu rabuwar hankali akan abun da ake nufi da rage darajar kudin kasa. Banbancin ya kaiga matsala mai girma. Yace matsalar ita ce an bar tattalin arziki a ofishin mataimakin shugaban kasa maimakon a ofishin shugaban.
Malam Hassan Gimba mai sharhi akan alamuran yau da kullum a Najeriya yace furucin Sarkin Kano na bisa hanya. Yace ya fadi gaskiya. Abin da ya kashe Najeriya shi ne manya basa fadawa gwamnati gaskiya watakila saboda wasu bukatu. Amma Sarki Muhammad Lamido Sanusi II an sanshi mai fadin gaskiya ne komi dacinta, kuma baya duba kansa sai dai kasar Najeriya.
Yace a duba duk wasu abubuwan gwamnati an kara masu kudi. Makarantun gwamnati an kara kudinsu kuma ko littafi daya basu sa a makarantun ba. Kudin abinci a kasuwa ya tashi. Darajar Nera ta karye.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.