A zaman kotun na yau, lauyan gwamnati Rotimi Jacob da mai kare shugaban Majalisar Dattawan, Joseph Daudu sun yi zazzafar muhara kan rashin bayyanar sanata Saraki bayan alkawarin da aka yi n a cewa zai halarci zaman kotun na yau.
“Abin takaici ne da ya ki bin umurnin kotun domin kuwa shi mai yin doka ne, bai kamata a ce ya tsallaka abin da doka ta gindaya ba.” In ji lauya Jacob.
Sai dai lauyan Saraki ya nemi ya wanke kansa bisa rashin bayyanar shugaban Majalisar inda ya ce ya dauka hurumin kawo shi (Saraki) ya koma kan shugaban ‘yan sanda da kotu ta bashi umurnin gurfanar da Saraki.
“Daga Juma’a zuwa yau, ni ina sauraran waya a ce min shugaban ‘yan sanda ya riga ya aiwatar da odar da aka bashi, tunda babu wanda ya yarda ni in zo da shi da kaina. Sai kawai ana so a ce na riga na ce zan kawo shi.” In ji lauya Daudu, a zantarwarsu da wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda.
Ana tuhumar shugaban majalisar ne bisa zargin cewa ya ba da bayanan da ba daidai ba kan kadarorin da ya mallaka.
A yau kotun dai ta cika makil da masu sha’awar su saurari karar, sai dai rashin bayyanar Bukola Saraki ya sa aka zaman ba tare da shi ba, inda yanzu haka, kotun tabbatar da da’ar ma’aikata ta jarjirce lallai sai shugaban ‘yan sanda ya tiso keyar shugaban majalisar dattawan a gobe.
Your browser doesn’t support HTML5