Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Zabe, Da Sauran Rina A Kaba -Masu Sharhi

INEC

masana kimiyyar siyasa da masu sharhi na cewa akwai sauran rina a kaba, bayan sanya hannu da shugaba Buhari ya yi kan sabuwar dokar zabe.

Wannan dari-darin ya shafi sake bukatar da shugaban ya yi ne na a goge sashe 84 na dokar da ya haramtawa masu rike da kujerun siyasa damar zaben ‘yan takara ko tsayawa takarar.

Fassarar wannan sashe na nuna mai son takarar mukami sai ya ajiye kujerar kafin samun damar yin hakan, inda shugaba Buhari ke da matsayar hakan rashin yin adalci ga wadanda ke wannan aji kuma ya sabawa tanadin tsarin mulki.

A hirar shi da Muryar Amurka, masanin kimiyyar siyasa Dr.Farouk BB Farouk ya ce ‘yan majalisar na da hurumin kyale dokar a yanda ta ke ko goge sashen, amma bisa fahimtar juna tsakanin fadar da majalisar.

Shi kuma mai gagarumin hamayya da tsarin gwamnatin APC Injiniya Buba Galadima wanda a lokutan baya ya rantse cewa, shugaba Buhari ba zai sanya hannu a dokar ba, ya ce har yanzu shugaban bai sanya hannun da zuciya daya ba kuma dama ya fara batun ne da dokar da shugaban ya mayar majalisa.

‘Yan siyasar APC da kan su irin jigon ta Musa Abubakar Danmalikin Kebbi sun yi kira ga shugaban ya sanya hannu kan dokar ba tare da cire wasu sassa da su ka

Da alamu dai majalisar mai shugabancin da ke biyayya sau da kafa ga shugaban ba za ta gwale shugaban ba ko da za a zarge ta da zama ‘yar amshin shata.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Zabe, Da Sauran Rina A Kaba -Masu Sharhi