Sarki Sanusi II Ya Bukaci Fulani A Ghana Da Su Dau Matakin Shari’a Kan Matsalolin Da Suke Fuskanta

Sanusi Lamido Sanusi II Ya Bukaci Al’ummar Fulani A Ghana Da Su Dauki Matakin Shari’a Kan Matsalolin Da Suke Fuskanta

Tsohon sarkin Kano kuma shugaban kungiyar Fulani ta duniya, Tabital Pulaaku, Sanusi Lamido Sanusi II, ya yi kira ga al’ummar Fulani a Ghana da su dauki matakin shari’a kan mutane da gungu da suke yi musu lakabi da zalunci ba bisa ka’ida ba.

Da yake jawabi a wajen wani taro da kungiyar Tabital Pulaaku reshen Ghana, da wasu kungiyoyin fararen hula suka shirya a birnin Accra, shugaban ya jaddada muhimmancin tsayawa tsayin daka wajen yaki da wariya da nuna kabilanci a dokance.

Kungiyar Fulani, Tabital Pulaaku ta duniya reshen Ghana ta shirya wannan zama ne domin mika korafinsu ga shugabansu, Halifa Sanusi Lamido Sanusi na II, na tsangwama, banbanci da hare-haren da suka ce suna fuskanta Ghana.

Sanusi Lamido Sanusi II Ya Bukaci Al’ummar Fulani A Ghana Da Su Dauki Matakin Shari’a Kan Matsalolin Da Suke Fuskanta

Babban Sakataren kungiyar a Ghana, Yakubu Musa Barry, da yake zayyana irin matsalolin da suke fuskanta yace “a matsayina na babban sakatare fiye da tawon shekaru goma, na zagaya ko ina a cikin kasar nan inda na shaida kalubalen da ’yan’uwanmu Fulbe suke fuskanta."

Ya ci gaba da cewa "babu lokaci mai yawa, zan yi jawabi na, amma zan ba ka takardun da za ka duba in ka samu lokaci. Idan muka ce za mu fara bayyana batutuwa ko kalubalen da muke fuskanta zai kai mu ga dare”.

Sanusi Lamido Sanusi II Ya Bukaci Al’ummar Fulani A Ghana Da Su Dauki Matakin Shari’a Kan Matsalolin Da Suke Fuskanta

Sakataren ya yi tsokaci kan banbanci da ake nuna musu, yadda ake yawan alakanta muggan laifuka gare su, da kuma hana su ‘yancin zama ‘yan kasa da sauransu.

Sanusi Lamido Sanusi II ya yi wa Muryar Amurka bayani a gefen taron cewa, ya tunawa ‘yan uwansa Fulanin Ghana cewa matsalolin da suke fuskanta, su ne irin wadanda sauran Fulanin Sahel ke fuskanta.

Ya ce “ba zai yiwu da tashin hankali ba. Ya kamata su dauki kan su a matsayin ‘yan kasa, kuma su san cewa akwai hanyoyi da tsarin mulki na kasa da ake bi domin a warware wadannan matsaloli. Idan an samu shaidar zalunci, to a bi hakki har zuwa makura, kada a bari”.

Sanusi Lamido Sanusi II Ya Bukaci Al’ummar Fulani A Ghana Da Su Dauki Matakin Shari’a Kan Matsalolin Da Suke Fuskanta

Taron ya sami halartar shugabannin Fulani a Ghana da kuma wakilcin Fulani daga sauran bangarorin kasar. Wasu daga ciki sun yi tsokaci kan zaman.

Shaikh Dokta Lamido Jibril Sissy, daya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar Tabital Pulaaku a Ghana, kuma shugabanta na farko, yace ya gamsu da jawabin da shugaba Sanusi II ya yi, domin ya farkar da Fulanin ta hanyar bayyana musu hanyoyin neman hakkin kai a hukumance.

Shugaban majalisar sarakuna Fulani na Ghana, Sarki Muhammad Iddris Bingel a nasa bangaren, ya yabawa mai girma shugaban Tabital Pulaaku. Yace duk shawarwarin da ya ba su, za su yi nazari kuma su dabbaka.

Wazirin sarkin Fulanin yankin Accra, Alhaji Osman Garba ya yaba da kira da Shugabansu, Sanusi na biyu ya yi kan amfani da doka wajen warware matsalolin

A karshe Shugaban kungiyar Tabital Pulaaku ta duniya, Sanusi Lamido Sanusi II ya shawarci al’ummar Fulani da cewa, “mu ma mu duba kanmu, akwai Fulani masu laifi. Dukkanin mai laifi kamat ya yi da kanmu, mu dauke shi mu danka shi hannun hukuma, idan kuma mutum ya yi laifi, an zo kama shi, kuma mun tabbatar ya yi laifi kada mu kare shi. Za mu kare wanda bai yi laifi ba a cikinmu, za mu kare wanda aka zalunta, amma bai kamata mu taimakawa wanda shi ne ya yi zalunci ko wanda ya yi laifi ba”.

Saurari rahoton Idris Abdullah a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Sanusi Lamido Sanusi Ii Ya Bukaci Al’ummar Fulani A Ghana Da Su Dauki Matakin Shari’a Kan Matsalolin Da Suke Fuskanta.