Sanatocin Jihohin Arewa Sun Koka Kan Tabarbarewar Tsaro

A Najeriya, Sanatocin Jihohin Arewa sun koka kan sha'anin tabarbarewar tsaro a yankin. Wanan ya biyo bayan wani taron gaggawa ne da suka yi a Majalisar. To sai dai masu ruwa da tsaki na cewa kukan Sanatocin ihu ne bayan hari.

Sanatocin Arewan sun kwashi sa'o'i biyu suna ganawa cikin sirri, daga bayan taron sai Shugaban Kungiyar Sanata Aiyu Magatarda Wamako ya yi wa manema labarai bayani yana cewa Sanatoci na cikin tashin hankali da kuma halin damuwa kan yadda rashin tsaro ya ta'azzara a kasa har yake neman ya gagari Kundila.

Sanata Wamako ya ce dukan su Sanatocin Arewa sun hada kai, sun yi magana da murya daya saboda haka sun dauki hutu na tsawon makonni biyu, kuma kowannen su zai tafi tushen sa ya yi nazari da tuntuba akan wasu hanyoyi ko dabaru na daban da za a iya amfani da su wajen shawo kan al'amarin.

Shi kuwa daya cikin Sanatocin Arewan daga Jihar Neja Mohammed Sani Musa ya ce baya ga korafin Sanatocin Arewan, Majalisar Dattawan kanta ta sha yin Kudurori akan batun tsaron kasar bila'adadin amma duk ba su yi wani tasiri ba. Saboda haka yanzu da suka hada kawunansu za su tafi su yi nazarin mataki na gaba, to ko me yasa ba sa tsawata wa bangaren gwamnatin tunda su ne masu sa ido a harkar gudanarwa? Sanata Sani ya ce suna tsawata wa, sai dai yan adawa ne ba sa ganin haka.

Amma ga kwararre a fanin kimiyar tsaro na kasa da kasa Dokta Yahuza Ahmed Getso yana ganin wadan nan bayanai da yan majalisar dattawan suka yi ihun ka banza ne domin su ne ya kamata su sa ido akan yadda ake gudanar da kudaden da ake kashe wa a fanin tsaro wanda rahottani suka nuna cewa an riga an fitar da kudi da aka ba bangaren tsaro kusan Naira triliyan biyu. Dokta Yahuza ya ce yan majalisan ba su da kishin kasa kuma ba aikin da ya kai su suke yi ba.

A bangaren Majalisar wakilai ma labarin iri daya ne domin akwai dokar da majalisar ta riga ta yi wa karatu na biyu da ke neman sauya yadda sojojin ke gudanar da aiyyukan su ta yadda bangarorin uku na sojojin mu za su iya aiki tare yadda ya kamata domin shawo kan kalubalen tsaron da kasa ke fuskanta.

Saurare cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Sanatocin Jihohin Arewa Sun Koka Kan Tabarbarewar Tsaro