Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Fara Nazari Kan Kundin Kasafin Kudin 2021


Buhari yana sa hannu a kasafin kudin 2018.
Buhari yana sa hannu a kasafin kudin 2018.

Majalisar Dokokin Najeriya ta fara nazari akan Kundin Kasafin Kudin shekara mai zuwa domin gudun irin koma baya da aka yi ta samu a baya wajen tantance kasafin wanda ya sa ake samun jinkiri wajen aiwatar da shi kamar yadda ya kamata.

Muhinmin aiki a bitar kasafin Kudin shi ne kira da kwamitocin Majalisar ke yiwa shugabanin Hukumomi da ma'aikatun Gwamnati daya bayan daya suna kare kasafin ma'aikatun su wanda yakan taimaka wa Majalisar wajen tantance wasu batutuwan da aka kiyasta cikin kasafin.

Majalisar ta bayyana cewa, a wannan shekarar tilas ne manyan jami'an gwamnati su mika wuyansu ta wajen bayyana a majalisar domin amsa tambayoyin kan sha'anin kasafin kudin da aka ware wa ma'aikatunsu a wanan lokaci akasin abinda ake samu a lokutan baya.

Bisa ga dukan alamu za a iya cimma wannan burin kasancewa shugaba Mohammadu Buhari ya yi umurni cewa lallai shugabanin hukumomi su halarci zaman komitocin Majalisar da kansu ba wai su yi aike ba. Majalisar ta bayyana niyar kin amincewa da kasafin kudin irin wadannan hukumomin domin ya zama ishara nan gaba.

taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade
taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

A lokacin da yake yi wa Muryar Amurka karin haske akan matakin hukunci da Majalisar za ta dauka ga shugaban hukumar da ya ki halartar zaman kare kasafin sa, Sanata mai wakiltan Jihar Neja ta Gabas Mohammed Sani Musa ya ce dabi'ar kin halartar kiran da aka saba yiwa shugabanin hukumomin gwamnatin abin damuwa ne.

Ya ce wannan na cikin damuwar yan majalisar a kokarinsu na samun tantance alkaluman da ke cikin kasafin da irin ayyukan da za a yi wa kasa kuma hakan yana kawo koma baya wajen kammalla aikin kasafin, amma yanzu majalisar ta kuduri anniyar hukunta shugaban da bai zo kare kasafin sa ba inda za a bashi kudin aiwatar da kananan aiyuka ne kawai, a hana shi kudin yin manyan aiyuka.

fashin-bakin-masana-akan-kasafin-kudin-najeriya-na-2021

najeriya-yan-kasar-sun-bayyana-ra-ayoyinsu-kan-rage-kasafin-kudin-bana

ina-aka-kwana-kan-batun-kasafin-kudin-badi-da-buhari-ya-gabatar

Majalisa ta dauki mataki na gama aikin kasafin kudin badin kafin su tafi hutun watan Disamba na bana kuma ana sa ran Shugaba Mohammadu Buhari zai sa hannu a kasafin domin a fara aiwatar da shi a watan Janairu na badi.

Ya zuwa yanzu dai Majalisar dokoki ta riga ta yi wa kundin kasafin kudin karatu na biyu wanda ya ke nufin an kai sigar da Shugabanin Hukumomin zasu fara kare kasafin ma'aikatunsu.

Ranar asabar da ta gabata mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo ya bayyana hanyoyin da gwamnati zata bi na samun kudin da zata aiwatar da kasafin kudin shekara ta 2021 da suka hada da ciwo bashi, da saida wadansu kaddarorin gwamnati, da kuma zuba jafi a fannin gina rukunin gidaje da gwamnati zata samun kudin shiga.

Tuni masu kula da lamura suka fara kushewa matakan da gwamnatin ta ce zata dauka na samun kudaden musamman bashin da ta ke niyar ciwo wa da suke ganin daukan wannan matakin a lokutan baya bai sauya rayuwar talakawa ba banda kara nawaita wa kasar.

sai-an-ci-bashi-kafin-a-iya-aiwatar-da-kasafin-kudin-2021---sanata-abdullahi

buhari-na-neman-majalisa-ta-ba-shi-iznin-ciwo-bashin-dala-biliyan

basussukan-da-ke-kan-najeriya-sun-kai-naira-triliyan-31

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kudin shekara ta 2019 a watan Afrilu watanni biyar bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da shi. Jinkirin ya biyo bayan takun saka da aka rika yi tsakanin majalisar da hadiman gwamnati da aka bukaci su bayyana yadda za a kasafta kudin. An kuma zargi majalisar da shigar da Karin kudi a kasafin ta bayan fage domin biyan bukatun kansu inda aka zargi majalisar da kara Naira biliyan 86 a kan kasafin kudin da shugaba Buhari ya gabatar wa majalisar.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda cikin sauti:

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Fara Nazari Kan Kundin Kasafin Kudin 2021-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG