Dokar dai kwaskarima ce ga dokar da ake da ita yanzu wacce ke cewa a rufe duk wanda aka sama da aikata laifin na tsawon shekaru goma.
Sanata Oluremi Tinubu wacce ke wakiltar Legas ta tsakiya ce ta nemi a yi wa dokar wannan kwaskwarimar.
Wannan sabon sauyin ya faru ne bayan wani kwamitin kare hakkin dan adam na majalisar ya gabatar da wani rahoto wanda sanata Opeyemi Bamidele na jihar Ekiti ya jagoranta.
A jawabinsa, Bamidele ya ce yadda ake yin garkuwa da mutane a Najeriya ya fara yawa. Ya kuma jaddada kan yawan mutanen da ke rasa rayukansu a kullum.
A cewar Bamidele, "dole ne a sauya dokoki domin su zo dai-dai da laifukan da mutane ke aikatawa."
Majalisar ta kuma soke bambanci tsakanin maza ko mata kan laifin fyade.
Wannan sauyin na zuwa ne a lokacin da ake kara samun adadin wadanda 'yan bindiga ke garkuwa da su, musamman ma a arewacin Najeriya.
Facebook Forum