Ayogu, wanda ya kasance a Majalisar Dokoki ta kasa tsakanin 2007 zuwa 2015, ya rasu ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, a wani asibitin Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya.
A tsawon shekaru takwas da ya yi a Majalisar Dattawa, Eze ya kasance mamba a kwamitin tsara kundin tsarin mulki da gyara wanda ya yi wasu sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Bayan sake zabensa a Majalisar Dattawa a 2011, an nada shi shugaban kwamitin ayyuka na Majalisar Dattawa.
Sanata Ayogu, ya kuma yi aiki a matsayin memba na kwamitocin harkokin ‘yan sanda, tsare-tsare na kasa, sufurin ruwa da kuma al’amuran gwamnatin tarayya.
An haifi Sanatan ne a ranar 23 ga Nuwamba 1958, an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Enugu ta Arewa a jihar Enugu, inda ya karbi mulki a ranar 5 ga Yuni, 2007.