ZABEN2015: Sanarwar Boko Haram ta Zama Sabon Darasi

Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram yayinda yake magana a sabon faifan bidiyon da ya fitar.

Sanarwar da shugaban Boko Haram yayi ta zama daratsin da 'yan siyasa na muhawara akai.

Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram yayi sanarwa a wani faifan bidiyo cewa kungiyarsa zata tarwatsa duk wani shirin gudanar da zabe.

Sanarwar ta zama wata sabuwar daratsi da 'yan siyasa ke magana akai musamman wadanda suka fito daga arewa maso gabas inda kungiyar Boko Haram din tafi karfi.

Idan manufar sanarwar ta Abubakar Shekauta ya razana 'yan siyasa ne to bisa ga duk alamu bai yi nasara ba domin duk sun dage sai an gudanar da zaben watan gobe. Sun nuna cewa sadakarwa ce kadai zata ceto dimokradiyar Najeriya daga rugujewa, abun da dukansu suka kuduri yi.

Dan takarar PDP na Borno Muhammad Imam yace matsalar tsaron ka iya samun nasaba da halin 'yan siyasa. Yace da baya yadda akwai hannun 'yan siyasa a lamarin 'yan Boko Haram amma yanzu yana ganin akwai alamun gaskiya. Amma ya kira duk wani dan siyasa dake da hannu a ciki ya yiwa Allah ya dubi halin da kasar ke ciki. Idan lamarin bai shafeshi ba ya shafi wasu 'yan uwansa da kuma wasu na kusa dashi.

Shi kuwa dan takarar kujerar gwamna a jihar Gombe a inuwar APC Inuwa Yahaya yana ganin ko ma babu batun zaben, fitinar taki karewa. Yace duk wanda ya kawo wata barazana yana yi ne domin cimma wasu bukatunsa na daban. Bai makata barazanar ta karya gwiwar kowa ba. Yace mutane su fito su yi zabe domin babu inda ba'a yiwa mutane barazana, walau a wurin aiki ko gida ko wurin ibada. Idan an kawo shugabanci nagari duk matsalar rashin tsaro zata kau.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Sanarwar Shugaban Boko Haram Ta Zama Sabon Daratsi - 2' 30"