Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara a Taraba Sun Kai Harin Ta'addanci


Daya daga cikin hotunan harin ta'addanci
Daya daga cikin hotunan harin ta'addanci

Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kai hari a Jihar Taraba a Najeriya

Wasu mahara da ake zargin sun ketaro ne daga Jihar Filato sun kai hari a garuruwan Ibbi da Garin Lamido dake Jihar Taraba inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kona gidajensu. Wani shaidar ganin da ido ya fadawa wakilin Murya Amurka Ibrahim Abdulazeez cewa, ‘yan kabilar Tarok ne suka farmaki garuruwan tare da kona kauyukan.

Sai dai mai magana da yawun kabilar Tarok Mista Jangla Labot yace ba haka abin yake ba domin kuwa ba wani abinda ya hada su da mutanen wadannan garuruwa balle su kai musu hari. Ya nuna wannan kawai zargi ne da kuma kazafi irin na jama’a akan abinda ba su tabbatar da shi ba.

Dan Majalisa Ishaya Daniya ya nuna yadda abin ke ci musu tuwo a kwarya inda yace majalisar jihar Taraba zata dauki matakin gabatar da wannan matsala a gaban majalisarsu don sanar da duniya halin ake ciki. Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba sun nuna cewa suna iya kokarinsu don ganin ba a kawo ire-iren wadannan harin. Har yanzu dai ana samun tura ‘yan sintiri akan iyakokin Jihar don dakile wadannan hare-hare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG