Sana'oin Naira Goma-Goma Da Mata Ke Rainawa Ke Tada Jari-Nafisa

Nafisa Atta

Nafisa Atta wacce ta ce babban burinta ta ga mata sun sami daukaka tare da yin wasu sana’oin dogora da kai domin zama masu dogaro da kai, inda ta bukaci mata su daina raina sana’a.

A cewarta sana’ar Naira goma goma da matake raina wa ita ke tada jari har ya kai ga tarin dukiya da dama.

Nafisa Atta, ta ce a yanzu tana Facility management Company a Abuja ' bayan nan ta na aikin dafa abinci da gyaran jiki ga mata tare da amfani da wasu kayan gyara jiki irinsu kurkur da wasu kayan sa fata tayi sheki.

Ta ce ta karanci international studies, ne a jami'ar Ahmadu Bello University dake Zaria, inda a farko ta so ta karanci aikin likitanci amma hakar ta bata cimma ruwa ba, kuma ta ce ta shafe shekara guda bayan kammala karatu kafin ta samu aiki.

Nafisa ta ja hankalin mata da su jajirce wajen neman ilimi ta kuma kara da cewa ba dole ne sai mace ta sami digirin ba ko da diploma ne da zarar da ta sami ilimi na gaba da sakandire zai taimakawa al’umma ya kuma taimaka wa mace ita kanta. Ta ce ko adini ya ba mace damar samun ilimi domin ta kyautata al’ummar ta.

Your browser doesn’t support HTML5

Sana'oin Naira Goma Goma Da Mata Ke Rainawa Su Ke Tada Jari