A yau dandalinVOA sami bakucin malama Tasidi Sa’id Zakari malamar makaranta wacce ta fara karatu tun daga tushe har ta cimma muradin ta na kammala karatun ta na digiri.
Ta ce ta yi karatun koyarwa irin na da bayan ta sami horaswa a pivotal teachers college, inda ta kware a fannin Home economics, wato ilimin girke girke, ta fara koyarwa bayan ta kammala karatu kuma yi aure.
Malama Tasidi ta ce ta fuskanci kalubale, a cewarta bayan ta sami gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, karatun bai zo da sauki ba duba da yawan zirga zirga daga Kano zuwa Zaria, ga dawainiyar gida da ‘ya’ya ga kuma na mai gida.
Ta kara da cewa a da ba’a bada damar koyarwa har sai an tabbatar da ka cancanta, sabanin yadda ake yi a yanzu inda aka siyasantar da harkar koyarwa.
Harkar karatun da, na da yanzu akwai banbamci duba da irin yanayin malaman da ake samar wa a yanzu, ta ce hanya daya da za’a kawo sauyi a harkar karatun zamani a Najeriya sai an koma baya yadda ake yi a da a
Daga karshe ta ce malaman da ake dauka a yanzu basu cancanta ba, ta bukaci gwamnati ta shigo cikin harkar ilimi ta hanyar tabbatar da an inganta makarantu ta hanyar sanya masu kayan aiki yadda ya kamata.
Ta kuma ja hankalin mata da su jajirce wajen neman ilimi, domin baiwa 'ya’ya tarbiya, domin ita ce kadai hanyar da za’a dawo da martabar al’umma.
Facebook Forum